An bayyana matakin da Kotun kolin tarayya ta dauka na ba wa ?ananan hukumomi ‘yancin gashin kansu da hana gwamnoni yi musu katsalandan, da cewar mataki ne na nasara kuma abin a yaba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar PDP na Jihar kaduna, kuma ?an takarar Shugabancin jam’iyyar a jihar Mr Edward Auta, a yayin wata ganawa da suka yi da wakilinmu a Kaduna.
?an Siyasar ya kara da cewar sai dai wani hanzari ba gudu ba, ya kamata a fa?a?a al’amarin ya zuwa ga za?ukan ?ananan hukumomi, ya zamana an cire za?ukan daga gwamnatin jihohi zuwa hukumar za?e ta kasa INEC.
“Idan kayi la’akari za kaga cewa kasancewar harkar gudanar da za?ukan ?ananan hukumomi na hannun jihohi shi ya sa a duk lokacin da aka gudanar da za?e sai ace jam’iyya mai mulki ita ce ta lashe dukkanin kujerun kananan hukumomin, kuma kowa ya sani ‘yan amshin shatan gwamna ne kawai ake zaba, saboda haka koda ya zamana an tsame gwamnonin daga harkar ku?in ?ananan hukumomi amma duk da haka zai kasance yaran sune a shugabancin ?ananan hukumomin, kaga an gudu ba a tsira ba kenan, an baka kyauta da hannun dama an kwace da hannun hagu”
