Ministan Harkokin Noma na Nijeriya Mohammad Abubakar ya ce Saudiyya ta nuna sha’awar fara shigar da ton 200,000 na naman shanu da ton miliyan ?aya na waken suya cikin ?asarta duk shekara daga Nijeriya.
Minista Mohammed ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa Saudiyya ta nuna sha’awar hakan ne bayan da Ministanta na Harkokin Noma ya ziyarci Nijeriya tare da yin wasu taruka da ‘yan kasuwa a fannonin noma.
“Nuna sha’awar tasu kan wannan batu ke da wuya sai muka fitar da wani tsari da za mu iya samar da yawan abin da suke so da kuma biya musu bu?atarsu,” a cewar Ministan Harkokin Noman na Nijeriya.
Ya ?ara da cewa dama Nijeriya na neman abokan hul?a na kasuwanci don samun ku?a?en ?asashen waje bayan da ta sha fama da ?arancin dalar Amurka, lamarin da ya yi mummunar illa kan tattalin arzikinta da kuma rage darajar kudin ?asar na Naira sosai.
Nijeriya ta da?e tana son raba ?afa kan harkokin fitar da kayayyaki zuwa ?asashen waje, maimakon fitar da ?anyen man fetur kawai, wanda a yanzu fitar da shi shi ka?ai ba ya iya ri?e tattalin arzikinta sosai.
