Kano: Abba Gida-Gida Ya Kafa Kwamitin Bincikar Ganduje

images 2024 03 06T195109.222

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya kafa kwamitoci biyu na binciken sayar da kadarorin gwamnatin jiha, rigingimun siyasa da kuma binciken ?acewar wasu mutane da aka daina jin ?uriyar su daga 2015 zuwa 2023.

Da ya ke ?addamar da kwamitocin a ranar Alhamis, Gwamna Abba ya sha alwashin sai an hukunta duk wani da aka samu da hannu wajen aikata laifi ko laifukan da za a binciko.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Ya?a Labaran Gwamna, Sanusi Bature ya fitar a ranar Alhamis, gwamnan ya tunatar wa kwamitin binciken salwantar Kadarorin cewa binciken wannan bada?ala na ?aya daga cikin al?awurran da ya ?auka a ranar da aka rantsar da shi.

“Hargitsin siyasa na daga cikin abin da ke kawo koma-baya a dimokra?iyya duk duniya. Kuma shi ne ke kai ga asarar rayuka da dukiyoyi da rashin amannar da talakawa ke yi wa masu mulki.”

“Akwai munanan rikice-rikicen da suka haifar da rasa rayuka musamman a 2023, wa?anda ba za a ba su baya a manta da su ko a binne su ba. Za a binciko su domin tabbatar da irin haka ko makamancin hakan bai sake faruwa ba.”

Kwamiti na farko ya na ?ar?ashin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, shi ne kuma zai binciki rigingimun siyasa na 2015 zuwa 2023.

“Shi wannan kwamitin muna so ya binciko irin yadda aka ?ulla rikicin, sannan a banka?o wa?anda duk ke da hannu ko ma su wane, domin a hukunta su. Kwamitin zai banka?o musabbabin tashin rikice-rikicen a 2015, 2019 da 2023.”

Shi kuma kwamiti na biyu da ke ?ar?ashin Mai Shari’a Faruk Lawan, shi ne wanda Gwamna Abba ya ?ora wa nauyin bibiya da banka?o yadda aka sayar da kadarorin gwamnatin Kano.

Abba ya hori kwamitin da sauran ?aukacin mambobin sa kada su saurara ko jan-?afa wajen gano yawan kadarorin gwamnati da aka sayar, musamman lokacin gwamnatin da ya gada.

Ya ce a gano yawan kadarorin na gwamnatin Kano da aka salwantar a ciki da wajen jihar Kano.

Sai dai Gwamna Abba ya ce wannan gagarimin aikin da ya ?auko ba siyasa ba ce, kuma ba wasu ?ai?aikun mutane ya ke harin kamawa ba.

Ya ce nauyi ne da alar Jihar Kano ta ?ora masa, shi kuma zai cika al?awarin saukewa.

Gwamnan ya ba kwamitin watanni uku ya kammala bincike tare da mi?a masa rahoton sakamakon bincike.

Related posts

Leave a Comment