Da Dumi-Dumi: An Ceto Dukkanin Daliban Kuriga Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Jihar Kaduna

IMG 20240310 WA0186

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa Gwamnatin jihar ta bayar da rahoton cewa an sako duka ?aliban makarantar Kuriga da ?anbindiga suka sace.

An sace ?aliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ?auyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.

Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ?aliban kuma suna cikin koshin lafiya.

Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ?aliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ?aliban.

“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.

Galibinsu ?aliban da aka sace ?an shekaru biyar ne zuwa 18.

Wani malamin makarantar ta Kuriga mai suna Sani Abdullahi wanda ya ku?uce ya bayyana cewa an sace dalibai na bangaren sakandare 187, sai kuma bangaren firamare ?alibai 100.

Related posts

Leave a Comment