Bauchi: An Amince Da Amfani Da Harshen Hausa Wajen Gudanar Da Harkokin Majalisa

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewaMajalisar Dokokin jihar ta amince a rika amfani da harshen Hausa wajen gudanar da lamuranta. Kakakin majalisar dokokin, Abubakar Y Suleiman ne ya bayyana haka a zaman da ta yi a jiya Talata.

Majalisar ta lura da zunzurutun yawan masu amfani da harshen Hausa a jihar wajen kafa wannan sabuwar doka.

Kafun jihar Bauchi akwai jihohi da dama a yankin Arewa da suke amfani da harshen Hausa a majalisun dokoki.

Shin ko kuna ganin akwai wani tasiri ko amfani da yaren Hausa a majalisunmu na Arewa?

Related posts

Leave a Comment