Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai ya yi ?arin haske kan kalaman da ya yi ana dab da rantsar da sabuwar gwamnati
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa wasu ne kawai marasa son gaskiya suka sauya ha?i?anin ma’anar kalaman da ya yi a lokacin Ya nesanta kansa ce da fa?in Shugaba Tinubu da addini ya yi amfani wajen lashe mulkin shugabancin ?asar nan
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya nesanta kansa da cewa ya yi kalaman da ke cewa Shugaba Tinubu ya yi amfani da addini wajen cin za?en ?asar nan.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ?arya ce kawai tsagwaronta wacce aka ?ir?iro ake jifansa da ita, rahoton The Cable ya tabbatar.
Da yake magana a wajen ?addamar da wani littafi a wajen bikin ritayar Farfesa Ishaq Akintola na jami’ar jihar Legas, tsohon gwamnan ya ce ya ?i yin martani kan sauya masa kalamai da aka yi ne saboda wa?anda suka yi hakan basu son gaskiya.
El-Rufai ya bayyana cewa kalaman nasa da ya yi ana dab da rantsar da sabuwar gwamnati kan siyasa da mulki a jihar Kaduna da batun tikitin Asiwaju-Shettima kamata ya yi ace an fahimcesu da idon basira.
El-Rufai ya nuna godiyarsa kan wa?anda suka goyi bayansa a lokacin Tsohon gwamnan ya nuna godiyarsa ga ?ungiyar MURIC da sauran wa?anda suka ri?a kare shi ta hanyar bayyana ha?i?anin sa?on da yake nufi a cikin kalaman da ya yi a wancan lokacin, cewar rahoton
A kalamansa: “Na yanke shawarar ba zan ta?a martani kan mur?e gaskiya da ?arairayi na batun musuluntar da ?asa da ire-irensu saboda wa?anda ke yin wannan ?agen za su yi ta yi ne saboda basu ganin ?imar gaskiya da daidaituwa.” “
“Sun riga da sun gama yanke hukunci kan sa?on da wanda ya isar da shi ko da kuwa na yi magana ko ban yi ba.”
Tsohon Gwamna Ya Fasa ?wai “Ga wa?anda su ke son sanin gaskiya, sa?o na a Kaduna shi ne shugabanci yana ginuwa ne kan turbar gaskiya da adalci (a musulunci ko kiristanci), sannan dole shugaba ya yi adalci ga kowa, musulmi da kirista ko wanda ba haka ba.”
