Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ofishin yankin na hukumar yaki da karya tattalin arzikin kasa wato EFCC dake shiyar Sokoto ya bayyana cewar daga shekarar 2019 zuwa yau ya samu sama da mutane 2000 da tabbacin aikata laifuffukan cin hanci da rashawa a gaban kotuna.
EFCC, ta ce ta samu nasarori da dama wajen kawar da laifuffukan tattalin arziki da hada-hadar kudi a Najeriyar, da kuma fadada ayyukanta a sassan kasar, domin kakkabe wadanda ke yiwa arzikin kasar zagon kasa.
A wani labarin makamancin wannan wata ?ungiya ta bu?aci a karrama wani Jami’in Hukumar dake ya?i da cin hanci da rashawa tare da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC saboda kin kar?ar cin hanci na Naira Milyan Hamsin…..
Jami’in hukumar mai suna Abubakar Aliyu dai ya?i kar?ar cin hancin zunzurutun ku?i har naira Milyan Hamsin domin yayi watsi da tuhumar da hukumar take yima wani fitaccen ?an siyasa a jihar Kano.
A cewar ?ungiyar Abubakar yayi abun a yaba mashi ta hanyar ?in amincewa ya kar?i wa?annan ku?in a matsayin shi na wanda yake jagorancin rundunar bincike ta musamman a reshen jihar Kano.
?ungiyar mai suna Anti corruption and integrity forum ta ?ara da cewa Jami’ai irin Abubakar kamata yayi a ri?a karramasu domin ya zama izina ga sauran abokanin aikin ta hanyar nuna juriya jajircewa akan aikin su tare da gaskiya da ru?on Amana.
