Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattawan ?asar wata takarda da ke neman majalisar ta amince masa kar?o bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya domin rage ra?a?in da za a sha sanadin cire tallafin mai.
Hakan na zuwa ne bayan sanarwar gwamnatin tarayya cikin watan Aprilu na bayar da tallafin dala miliyan 800 na bankin duniya ga ?an Najeriya masu rauni su miliyan 50 ko gidaje miliyan 10.
A cewar ministar ku?i da kasafi da tsare-tsare ta ?asa, Zainab Ahmad, za a rarraba tallafin ne bisa shirin da aka yi na cire tallafin mai a watan Yunin bana.
Ministar ta ce ana ci gaba da aiki tare da sabon kwamitin mi?a mulki na shugaban ?asa da gwamnati mai jiran gado domin tafiyar da shirin da ya ha?a da bu?atar samar da bas-bas da wasu bukatu da dama.
