Sabuwar Gwamnati: Shawarata Ga Uwargidan Tìnubu – Turai ‘Yar’adua


Uwar gidan tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, Turai ‘Yar’adua ta bai wa matar shugaban ?asa mai jiran-gado Remi Tinubu shawara kan yadda za ta fuskanci harkokin ofishin matar shugaban kasa.

A hirarta da BBC Hajiya Turai ta ce matu?ar kina kan mu?amin (First Lady) to sai “kin yi ha?uri, saboda idan mijinki zai tsaya ya yi irin abin da Umaru ya yi, ya hana a yi ba daidai ba shi ma kuma ya ?i yin ba daidai ba, to ke za a ri?a zargi.

“Ni ma haka na zama, domin mijina ba ya shan giya ba ya neman mata, kuma ba a same shi da cin hanci ba,” in ji Turai.

Ta ?ara da cewa sai laifi ya koma kanta a matsayinta na matar shugaban ?asa, don haka babu abin da Remi za ta yi sai ha?uri.

“Babu wanda zai bai wa shugaban ?asa shawarar gaskiya sai matarsa, duk wanda yake zagaye da shi zai gaya masa abin da yake son ji ne kawai.

Turai ta ci gaba da cewa, “Za ta fa?a masa abin da ta ji ana fa?a ba tare da tsoro ba, kuma ta ba shi shawarar ya bincika domin tabbatar da gaskiya.”

Wani abu ne da aka saba da shi a ‘yan shekarun nan, yadda matan shugabannin ?asa ke taimaka wa mazajensu wajen cimma abin da suke nema yayin mulkinsu.

Ba kuma kawai a Najeriya ne hakan ke faruwa ba, har ma da kasashen duniya daban-daban.

Wasu daga cikin fitattun matan shugabannin ?asa da suka taka rawar a-zo-a-gani a mulkin mazajensu sun ha?a da, Hillary Clinton matar Shugaban Amurka Bill Clinton da ya yi mulki a ?arshen shekarun 1990.

Akwai Michelle Obama da Lalla Salma matar Sarkin Morocco da Chantal Biya matar Shugaban Kamaru da Margaret Gakuo Kenyatta matar tsohon Shugaban Kenya, Uhuru Kenyata.

A ranar 29 ga watan Mayun da ake ciki ne za a rantsar da sabon shugaban Najjeriya Bola Ahmed Tinubu.

Ana sa ran mai dakin nasa za ta taka rawar gani a mulkinsa, ganin cewa ita kanta ‘yar siyasa ce, wadda a baya ta taba zama sanata.

Related posts

Leave a Comment