Nadin Sarauta: Tinubu Ya Taya Sarki Charles Murna

A cikin wata wasi?ar taya murna da Tinubun ya aike wa Sarki Charles lll ya ce a shirye yake domin yin aiki tare da sabon sarkin.

Tinubu ya ce yana da ya?inin sarkin zai bi sawun mahaifiyarsa Sarauniyar Elizabeth ll, wajen kawo ci gaba a Birtaniya da ?asashen ?ungiyar rainon Ingila ta Commonwealth.

Za?a??en shugaban wanda ke jiran rantsuwar kama aiki, ya ce yana fatan dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya za ta ci gaba da ?arfafa a tsawon zamanin mulkin Sarki Charles lll.

”A matsayina na za?a??en shugaban Najeriya, ina fatan cewa a zamanin mulkinka, za a samu yau?a?ar dangantaka tsakanin Najeriya da Birtaniya domin ciyar da ?asashenmu gaba”, in ji Tinubu.

Daga ?arshe Tinubu ya yi addu’ar samun ?warin gwiwwa tare da nasara ga sabon sarkin a ilahirin tsawon mulkisa.

A ranar 29 ga wannan wata ne dai za a rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya bayan nasarar da ya samu a za?en shugaban ?asar da aka gudanar cikin watan Fabrairu.

Related posts

Leave a Comment