Zaben Gwamnan Kaduna: El-Rufa’i Na Shirin Kama Jagororin PDP A Kaduna – Makarfi

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ahmed Makarfi ya zargi gwamna Nasir El-Rufai na gwamnatin Kaduna da shirin tursasa ‘ya’yan jam’iyyar.

Makarfi ya ce gwamnatin El-Rufa’i na shirin kame wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar PDP bisa zargin shi na ?arya.

Ya yi zargin cewa shirin shi ne a yi amfani da jami’an tsaro wajen damke ‘ya’yan jam’iyyar PDP don kada su samu damar shiga zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da ke tafe.

Tsohon gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta gano ‘ya’yan jam’iyyar su 80 da ta ke shirin kamawa bisa wasu kalamai na tunzura jama’a.

Ya kara da cewa shirin shi ne a kama Manyan jami’an PDP da kuma raunana su gabanin zaben da za a yi a ranar 18 ga watan Maris mai zuwa.

Makarfi, ya bayyana cewa PDP ta riga ta mallaki jerin sunayen a hannunta, ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake mayar da martani kan kamun da aka yi wa daraktan yada labarai na majalisar yakin neman zaben PDP na jihar Kaduna, Saidu Adamu da wasu jami’an PDP guda biyu.

A cewarsa, “An jawo hankalinmu ga jerin sunayen jami’an mu da gwamnati ta tsara don kamawa da tsare su har sai an kammala zabe. Wannan yana da sakamako mai ban mamaki.

“Wadanda aka rubuta domin kama su, sun fito ne daga kananan hukumomin Kudan, Sanga, Igabi, Lere, Kachia, Jaba da kuma Kaduna ta Arewa da ke jihar wadanda ake kyautata zaton tungar PDP ce.

“Har yanzu Honourable Adamu yana tsare kuma ba mu san laifukan da ake zarginsa da shi ba, kuma ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba, wannan lamari ne mai ban takaici.

Related posts

Leave a Comment