Babban Banki Ya Amince A Cigaba Da Amfani Da Tsoffin Kudin ?500 Da ?1000

Sabbin rahotanni dake fitowa sun bayyana mana cewa, babban bankin Najariya, CBN ya amince a ci gaba da amfani da tsaffin kudaden Naira 500 da 1000.

Jaridar the Cable ta ruwaito cewa, bankunan Zenith, UBA, da GTB a Legas sun bayar da tsaffin kudaden Naira a yau.

Hakanan kuma wani jami’in daya daga cikin bankunan da jaridar ta zanta dashi ya bayyana cewa, sun samu umarnin yin hakan ne.

‘Yan Najeriya dai sun shiga cikin tashin hankali tsawon lokaci sakamakon karancin kudi da matakin da babban banki ya ?auka na daina amsar Tsoffin takardun ku?i ya haifar.

Related posts

Leave a Comment