Hukumar za?e ta ?asa ta cire sunan shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa daga cikin jerin sunayen za?a??eun ‘yan majalisar wakilan ?asar da suka yi nasara a za?en da aka gudanar cikin watan Fabrairu.
Hukumar za?en ?asar ce dai tun da farko ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a za?en ?an majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar maza?ar Doguwa da Tudunwada a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Jami’in tattara sakamakon za?en Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya bayyana cewa Doguwa na jam’iyyar APC ya samu ?uri’a 39,732, inda abokin takararsa na jam’iyyar NNPP Yushau Salisu Abdullahi ya samu ?uri’a 34,798.
To sai dai a jerin sunayen za?a??un ‘yan majalisun da hukumar za?en ta fitar a shafinta na Twitter, babu sunan Alhassan Ado Doguwa a cikin jerin ‘yan majalisun.
INEC ?in ta ce an tilasta wa jami’in tattara sakamakon za?en wajen bayyana sakamakon da ya bai wa Doguwa nasara a za?en da aka gudanar.
