Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Taya Tinubu Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?ungiyar ha?in kan ?asashen Musulmi ta taya sabon za?a??en shugaban Najeriya Bola Tìnubu murnar samun nasara a za?en da aka gudanar a ?asar ranar Asabar da ta gabata.

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban ?ungiyar Malam Hissein Brahim Taha, ya fitar mai ?auke da sa hannun daranktan ya?a labaranta Wajdi Sindi, wanda ya ce a madadin shi da mambobin baki ?aya suna aika sa?on taya murna ga Asuwaju Bola Ahmed Tinubu kan za?en da ya lashe.

Shugaban ya ce za?en da ‘yan Najeriya suka yi wa shugaban yardarsu ce suka ba shi game da burinsa kan Najeriya na ta zama ma?aukakiya, saboda kwarewar da yake da ita a rayuwa, zai lura da lamurn Najeriya domin tabbatar da ci gabanta da kuma bun?asarta.

Ya kuma jaddada muhimmancin da ?ungiyarsu ke da shi a ala?arta da Najeriya tare da ba da tabbacin ?arfafa ala?a ta hanyar ha?in kai ga Najeriya ta ko wanne bangare, musamman ta fanni ci gaban al’umma da kuma ya?i da ‘yan ta’add da masu tsattauran ra’ayi.

A ?arshe ya yi wa ?asar fatan alheri da kuma samun nasara mai ?orewa.

Related posts

Leave a Comment