Zargin Magudi: Kotu Ta Ba Atiku Da Obi Damar Bincikar Rumbun Hukumar Zabe

Kotun ?aukaka ?ara a Abuja ta bai wa ?an takarar shugaban Najeriya a ?ar?ashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na Labour, Peter Obi damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a za?en ranar 25 ga watan Fabarairu.

Tun farko ?an takarar ne daban-daban suka mi?a bu?atar neman a ba su damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a babban za?en 2023 tare da tilasta wa INEC ta ba su damar ganin kayan aikin da aka yi amfani da su a za?en shugaban ?asar.

A ranar Laraba 1 ga watan Maris ne Atiku Abubakar ya shigar da tasa ?arar yayin da Peter Obi kuma ya shigar da tasa ranar Alhamis biyu ga watan.

Kan haka ne kotun ta umarci hukumar za?e ta bai wa ?an takarar PDP damar duba kayayyakin za?en.

A yau Juma’a kuma kotun ta amsa bukatun ‘yan takarar na duba kayan za?en sannan kuma su titsiye hukumar za?e kan wasu bayanai da za su bu?ata.

Kotun ?ar?ashin mai shari’a Joseph Ikyegh ta bayar da umarnin ne bayan da ta saurari wasu ?ararraki da ?an takarar biyu suka shigar tare da jam’iyyunsu.

PDP da LP wa?anda a baya-bayan nan suka yi watsi da sakamakon za?en, sun ce samun damar ganin kayayyakin za ta taimaka musu a ?alubalantar sakamakon za?en da suke yi wanda ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.

A cewar INEC, Tinubu ya ci za?en ne da ?uri’u 8,794,726 inda Atiku Abubakar na PDP yake bi masa da ?uri’u 6,984,520 sai Obi na Labour Party da ya zo na uku da ?uri’u 6,101,533.

Related posts

Leave a Comment