Gwamnatin jihar Neja ta shigar da karar gwamnatin tarayya a dalilin tsarin da bankin CBN ya fito da shi na canza wasu takardun kudi, Neja ta zama jiha ta biyar da za tayi shari’a da gwamnatin Muhammadu Buhari a kan tsarin kudin.
Kwamishinan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin jihar Neja, Nasara Danmallam ya fitar da jawabi cewa sun kai kara gaban koli, yana cewa kararsu mai lamba SC/CV/210/2023 tana kotun koli tun a ranar Juma’a, su na sa ran a biya masu bukata.
Kwamishinan ya ce su na rokon babban kotun kasar ta tsawaita wa’adin da bankin CBN ya bada na canza N200, N500 da kuma N1000.
Lauyoyin Gwamnatin Neja sun sanar da Alkalan kotun cewa karancin sababbin takardun kudin ya jefa al’ummar jihar Neja cikin mawuyacin hali. Kamar yadda rahoton ya bayyana, mutanen karkara sun fi shan wahalar tsarin sauya kudin, don haka Kwamishinan ya ce suke neman ceton mutane.
A matsayinsa na Kwamishinan shari’a, Nasara Danmallam ya nuna gwamnatinsu za tayi duk abin da za ta iya domin ganin an raba jama’a da wahala.
