Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ‘yan sa-kai a dajin Yargoje cikin ?aramar hukumar Kankara a jihar Katsina.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ?asar Malam Garba Shehu ya fitar ya ce harin wanda ‘yan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar ‘yan sa- kan da dama.
‘Yan bindigar sun yi wa ‘yan sa-kan kwanton ?auta a dajin a lokacin da suke ?o?arin ?wato wasu shanu da aka sace.
Shugaban ?asar ya bayyana alhininsa kan rasuwar jami’an sa-kan tare da jajanta wa iyalansu, yana mai cewa Najeriya ba za ta manta da sadaukarwar da suka yi na kare ?asa, tare da ya?ar miyagun laifuka a ?asarsu ba.
“Muna addu’a tare da jajanta wa iyalan mamatan a wannan lokaci na alhini. Muna addu’ar Allah ya gafarta musu” in ji Buhari.
Jihar Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin ?asar na fama da matsalolin ayyukan ‘yan bindiga, wa?anda ke yawan kai hare-hare, tare da sace mutane domin neman ku?in fansa.
