Karancin Mai Na Iya Zama Barazana A Babban Zabe Dake Tafe – INEC

Hukumar Za?e Mai Zaman Kanta ta ?asa INEC ta ce matsalar ?arancin man fetur da ?asar ke fuskanta ka iya shafar tsare-tsaren hukumar game da za ta shirya za?en ?asar da ke tafe.

Shugaban Hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja a lokacin taron tuntu?a tsakanin hukumar da ?ungiyoyin direbobin haya na ?asar wa?anda suka ha?ar da NARTO da NURTW da sauransu.

“Hukumar za?e tana tare da ku game da kokenku na ?arancin man fetur da ?asar nan ke fuskanta, da yadda hakan zai shafi hakar sufuri musamman a ranar za?e,” in ji Mahmood.

Ya ?ara da cewa “magana ta gaskiya ita ce rashin wadataccen man zai shafi shirye-shiryenmu”.

Shugaban hukumar ya ce dangane da wannan dalili , hukumar za?e za ta gana da kamfanin mai na ?asa NNPCL domin duba hanyoyin da ya kamata a bi wajen magance wannan matsala.

Related posts

Leave a Comment