Buhari Ya Dawo Najeriya Bayan Halartar Taro A Murtaniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya koma gida bayan halartar taron zaman lafiya karo na uku da ?ungiyar zaman lafiya ta Afirka ta gudanar.

A lokacin halartar taron da aka gudanar a Mauritaniya, shugaba Buhari ya bayyana yadda gwamnatinsa ta kashe ku?a?e masu yawa wajen sake ?wato garuruwan da ke hannun maya?an Boko Haram a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Haka kuma shugaba Buhari ya ?ora alhakin rashin daidaitar al’amuran tsaro a ?asar da ma yankin tafkin Chadi kan rikice-rikicen da ake yi a ?asashen Libya da jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ma mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.

A wajen taron kuma Buhari ya kar?i lambar yabo ta ‘?arfafa zaman lafiya a ?asashen Afirka” wadda ?ungiyar wanzar da zaman lafiya ta Afirka ta ba shi.

Related posts

Leave a Comment