Da Dumi-Dumi: An Kulle Masallatai Da Makarantar Abduljabbar Bisa Umarnin Kotu

Gwamnatin Jihar Kano ta bi umarnin kotu, inda ta gar?ame masallatan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma makarantarsa.

Haka-zalika, bisa bin umarnin kotun, gwamnatin ta kuma kwace littattafan sa guda 189, inda ta kai su zuwa ?akin kararu.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a ranar 15 ga watan Disamba, Babbar Kotun Shari’a ta Kano, ?ar?ashin jagorancin Al?ali Ibrahim Sarki Yola, ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Hukuncin ya zo ne biyo bayan kama Abduljabbar da laifin furta kalaman ?atanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) a wasu karaturrukan sa.

Laifin ya sa?a da sashe na 382 da 375 na kundin shari’ar Kano na 2000.

Da ya ke yanke hukuncin, Sarki Yola ya kuma umarci gwamnatin Kano da ta rufe dukka masallatai da makarantar Abduljabbar, sannan ta kwace littattafan sa 189 da ya kafa hujja da su lokacin shari’ar.

Tuni dai gwamnatin ta cika wannan umarni, inda ta gar?ame masallacin nasa na Filin Mushe a Gwale da Jamiurrasul da ke sharada.

An ga kuma jami’an tsaro na shawagi a guraren masallatan da makarantar, inda tuni a ka aike da littattafan na sa zuwa ?akin karatu na jihar.

Related posts

Leave a Comment