Mr LA Ya Sha Kaye A Zaben Fidda Gwanin PDP Na Sanatan Kaduna Ta Tsakiya

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Ibrahim Usman, ya lashe zaben fidda gwani na ?an takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya karkashin inuwar jam’iyyar PDP, inda ya doke Lawal Adamu (Mr LA) wanda a baya aka ayyana matsayin wanda ya yi nasara.

Usman Ibrahim wanda tsohon shugaban ?aramar hukumar Kaduna ta arewa, ya tashi da ?uri’u 210 daga cikin 223 da aka ka?a wanda ya bashi damar lallasa abokan fafatawarsa 5.

Babbar Kotun tarayya dake zama a Kaduna ta rushe za?en fidda gwanin farko da PDP ta shirya a maza?ar Sanatan Kaduna ta tsakiya ranar 24 ga watan Mayu inda ta bada umarnin sake gudanar da sabon za?e.

Kotun ?ar?ashin jagorancin Mai shari’a Muhammad Umar ta rushe za?en farkon ne saboda saba wa doka da aringizon kuri’u kana ta umarci PDP ta sake sabon za?e cikin kwanaki 14.

Al?alin ya yanke hukunci ne biyo bayan ?arar da ?aya ?aga cikin ‘yan takara, Ibrahim Usman ya kai gabansa, yana kalubalantar za?en farko wanda aka ayyana Lawal Adamu a matsayin wanda ya samu nasara.

Bayan kammala sabon za?en wanda ya gudana ranar Litinin, shugaban kwamitin shirya za?en, Istifanus Mwansat, ya ayyana Ibrahim Usman a matsayin wanda ya zama zakara. Yace Usman ya samu kuri’u 210 daga cikin kuri’un Deleget 223 da aka tantance su ka?a kuri’unsu a tsakanin yan takara.

Lawal Adamu ya samu kuri’u biyar yayin da Farfesa Usman Muhammad Ya samu kuri’u biyu.

Related posts

Leave a Comment