Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Triliyan 42 – Hukumar Kula Da Bashi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sanarwar da gwamnatin tarayya ta bayar a wannan makon cewa za ta karbo karin bashin naira tiriliyan 11 domin tafiyar da kasafin kudin 2023 ya janyo muhawara a kasar.

Dokar harkokin karbar bashi ta nuna cewa karin bashin da Najeriya za ta karbo ya zarta adadin kudin da aka amince ta ranto.

Ministar harkokin Kudi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed wadda ta sanar da karbo bashin, ta ce za a karbo bashin ne daga cikin gida da kuma kasashen duniya.

Bayanai daga ofishin da ke kula da bashi da lamuni na Najeriya sun nuna cewa ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2022 jimillar bashin da ake bin kasar ya kai $100bn, kwatankwacin naira tiriliyan 42.

Najeriya ba ta taba jinginar da kadararta ba don karbo bashi
Kididdiga ta nuna cewa bashin da kasar ta karbo daga kasashen waje ya kai dala biliyan $40, kwatankwacin naira tiriliyan 17.

Kazalika ta karbi bashin biliyan $60, kwatankwacin naira tiriliyan 25 a cikin gida – wanda ya kunshi gwamnatin tarayya da gwanatocin jihohi da babban birnin tarayya.

Batun dai ya raba kawunan ‘yan Najeriya, inda wasu ke cewa babu laifi idan kasar ta karbo bashin muddin za ta yi amfani da shi wajen harkokin gina kasa.

Related posts

Leave a Comment