Labarin dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar tace bata kama wasu bakin haure a kasar nan suna rarraba makamai ta jirgin sama ga ‘yan bindiga a jihar ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Kurya ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna a ranar Juma’a cewa, lamarin bai taba faruwa ba a kowanne sashi na jihar ba.
Kurya ya kwatanta rahoton da labarin bogi dake yawo a soshiyal midiya saboda bai taba faruwa a jihar ba, inda ya yi kira ga jama’a da su yi fatali dashi.
“Ba mu kama wani ‘dan kasar waje da helikwafta yana raba makamai ga ‘yan bindiga ba yankin da muke kula da shi.” ”Abinda muke bukata daga jama’ar kirki shine bayanai masu amfani kan kai da kawowar miyagu, ballantana a yankunan kauyuka domin dakile annobar garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da satar shanu,”
Kwamishinan yace ‘yan sanda zasu cigaba da mayar da hankali wurin ganin bayan makiyan al’umma domin tabbatar tsaro. Kurya yayi kira ga ‘yan kasa nagari da su kasance masu sanya ido tare da hanzarta kai rahoton duk abinda suka zargi ga hukumomin tsaro mafi kusa.
