Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Tashi Garin Mada

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Jama’ar Garin Mada na cigaba da tserewa daga garin bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a jiya.

Shaidu sun tabbatar wa BBC cewa ?an bindigan sun harbi mutum ?aya sannan suka tafi da wasu mutum hu?u baya ga ?umbin dabbobi da suka kora.

Sai dai shaidun sun ce sojoji na dakatar da mutane da ke tserewa domin barin garin, inda suke hana su ficewa, lamarin da ya jawo mazauna Mada ke zanga-zanga.

An tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara domin ji daga garesa amma bai amsa kiran wayar da muka yi masa ba.

Wannan hari dai, shi ne irinsa na uku a cikin kwana uku a jere da ?an bindiga ke kaiwa garin na Mada da wasu garuruwan makwabta.

Related posts

Leave a Comment