Labarin dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Fasinjoji goma sha takwas a wata motar bus mai daukar mutane 18 sun kone kurmus a wani hatsarin Mota da ya wakana a Gidan Kwano hanyar Minna-Bida a karamar hukumar Bosso da ke jihar.
An tattaro cewa motar ta fito ne daga jihar Lagas zuwa wani wuri da ba a sani ba amma dai hukumomi sun ce ta yiwu tana a hanyarta ta zuwa Kano ko jihar Sokoto.
Hatsarin wanda ya afku da misalin karfe 3:00 na tsakar daren Lahadi, ya wakana ne bayan motar ta yi karo da wata babbar motar daukar kaya da aka faka a hanyar kafin ta kama da wuta.
Kasancewar abun ya faru a lokacin da mutane ke bacci, an tattaro cewa ba a samu kai agaji ba har sai zuwa 5:00 na Asubah lokacin da mutane suka fara taruwa.
Fasinjojin sun babbake kurmus har ba a iya gane su, an tattaro cewa an ceto biyu daga cikin mutanen sannan aka kwashe su zuwa asibtin IBB inda daya daga cikinsu ya rasu yayin da dayan ke cikin mummunan yanayi.
Kakakin ‘yan sandan jihar Neja, DSP Abiodun Wasiu, ya tabbatar da lamarin cewa an binne mutanen a kusa da inda hatsarin ya afku.
