Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar kungiyar mata ‘yan jarida ta ?asa NAWOJ, ta yi kira ga jam’iyyun kasar da su duba yiwuwar zabo mata a matsayin mataimaka a zaben 2023.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun shugabarta ta kasa, Ladi Bala.
Ladi Bala ta bayyana cewar sun dauki matakin ne saboda “muna da mata gwanaye, masu ilimi da suka dace su taka rawa wajen kawo ci gaba a kasar nan.”
“Wannan kira da muka yi ya zama wajibi domin kuwa a matsayinmu na ‘yan jarida mun ga cewa ya kamata a kawo mata a sha’anin mulki da ci gaban kasa,” in ji ta.
A cewarta, sanya mata a cikin harkokin mulki zai inganta yadda ake gudanar da shi da kuma tabbatar da adalci, tana mai cewa “tun da Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin kasashen duniya kan mata, ya zama wajibi a ba su damar taka rawa a ci gaban kasar”.
