2023: Ni Nafi Kowa Cancantar Zama Shugaban Kasa – Ahmad Lawan

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban majalisar Dattawa kuma ?an takarar Shugaban ?asa a karkashin jam’iyyar APC Ahmed Lawan, ya bayyana cewar shi ne ya fi kowa cancantar zama shugaban ?asa a shekarar za?e ta 2023.

A cewarsa, ya shekara 23 a majalisa kuma a cewarsa yana da ?warewar da zai jagoranci Najeriya.

Ya bayyana cewa ko a ?asashen da suka ci gaba, akwai da dama daga cikin wa?anda suka zama shugaban ?asa da ?an majalisa ne inda ya ce hakan ya sa ya cancanci zama shugaban ?asa.

Ya bayyana cewa idan aka zabe shi, zai ?ora daga kan manyan ayyukan da shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi wa Najeriya

Ya kuma bayyana cewa irin dabarun da aka yi amfani da su wurin ya?ar ?an Boko Haram a Arewa Maso Gabas, za su yi amfani da irin wa?annan dabaru domin ya?ar ?an bindiga da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya

Related posts

Leave a Comment