Mataimakiyar Shugabar Kungiyar Mata Lauyoyi ta kasa reshen jihar Gombe Ma’omi Malin Abba, ta yi kira ga kungiyoyin fararen hula a jihar da cewa su jajirce wurin ganin an samar da tsauraran dokoki da za a yi amfani da su a jihar wajen hukunta masu cin zarafin jama’a musamman masu laifin fyade.
Malin Ma’omi Abba ta yi kiran ne zantawar ta da wakilinmu a ofishin ta tace samar da dokoki masu tsauri za su taimaka matuka wurin magance matsalar cin zarafin jinsi musamman ma fyade, lamarin da tace yana ?ara ?aruwa duk da kokarin masu ruwa da tsaki wurin magance matsalar.
Ta ?ara da cewa kungiyoyin fararen hula musamman masu ruwa da tsaki na bada gudummuwa wurin fadakar da al-umma shi yasa ta yi kira gare su domin ka da su gajiya wurin fadakar da al-umma a yi wa matsalar taron dangi domin magance ta da samun kyautatuwar al’umma.
