Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta na?a Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku don ya maye gurbin Babban Akanta na ?asa Ahmed Idris, wanda aka dakatar saboda zargin almundahanar ku?i da suka kai naira biliyan 80.
Wata sanarwa da fadar ta fitar a yammacin Asabar ta ce Mista Nwabuoku zai jagoranci ofishin babban akantan har zuwa lokacin da hukumar EFCC mai ya?i da cin hanci za ta kammala bincikenta kan Ahmed Idris.
Mista Nwabuoku mai shekara 60 ya fito daga JIhar Imo shi ne darakta a ?angaren ku?i na ofishin akantan yanzu haka.
Jami’an EFCC sun kama babban jami’in gwamnatin ne ranar Litinin da ta wuce bayan ya ?i amsa gayyata daban-daban da suka aika masa, a cewar hukumar.
