Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Sadarwa, Isa Pantami zai jagoranci taron Kungiyar Bayanai ta Duniya ta shekarar 2022 bisa nadin da Kungiyar Sadarwa ta Kasa da kasa (WSIS) ta 2022 ta yi masa.
Za a yi taron ne a hedkwatar Kungiyar Sadarwar ta Kasa da Kasa da ke Geneva cikin kasar Switzerland.
Kamar yadda takardar da hadimin ministan na bangaren bincike da ci gaba, Dr Femi Aduluyi ya saki ta nuna, an sanar da ministan batun nadin na shi ne ta wata takarda wacce babban sakataren ITU, Houlin Zhao ya aika masa.
An nada Pantami ne saboda jajircewarsa a hanyar bayanai da ilimin fannoni da kuma dagewarsa akan harkokin WSIS, kamar yadda Zhao ya shaida. Kuma sai da su ka yi bincike kwarai kafin su dauki matakin.
“Nadin Pantami ya bai wa Najeriya da kuma Nahiyar Afirka wata babbar dama ta taka rawa a bangaren WSIS a shekararta ta 2022 wanda an fara taron ne tun 2003 kuma an ci gaba da yi duk shekara.”
