‘Yan Najeriya musamman masu sharhi kan harkokin siyasa sun cika da mamaki a ranar Asabar, 7 ga watan Mayu, lokacin da suka ji cewa shugaban kungiyar kamfen din Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abdulmunin Jibrin, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.
Tun bayan nan, ana ta tattaunawa kan abun da hakan ke nufi ga siyasar babban jagoran jam’iyyar mai mulki na kasa wanda ke son darewa kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
Legit.ng ta tattaro akalla abubuwa biyar da sauya shekar Jibrin zai janyo gabannin zaben fidda gwani na APC da ma zaben shugaban kasa mai zuwa.
1. Ko shakka babu wannan hukunci na Jibrin ya dasa ayar tambaya kan jam’iyyar mai mulki wacce ke ikirarin lashe kusan dukkanin kujeru a zaben 2023, ciki harda na shugaban kasa.
Hakazalika, wannan sauya shekar ya dasa ayar tambaya na, ta yaya jam’iyyar APC ta warware rikicin cikin gidanta da kuma tausar fusatattun mambobinta a kasar?
2. Haka kuma, akwai shakku kan ko Tinubu zai cimma kudirinsa na son zama shugaban kasa yayin da babban baraka na farko ya kunno kai a jam’iyyar kafin zaben. Ya zama dole Jagaban ya kara kaimi sosai don tabbatarwa duniya irin karfin da yake da shi a APC da kuma tasirinsa a arewa.
Idan har yunkurin sasanci da Tinubu ke son yi tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Jibrin bai haifar da ‘ya’ya masu idanu ba kamar yadda ake sanya rai, abubuwa da yawa na iya kwabe masa.
3. Tinubu na iya rasa farin jininsa a arewa, idan ana magana kan yankin arewa, kasancewar Jibrin ya fito daga Kano, jihar da a cikinta ne Tinubu ya shahara kuma yake da masoya, idan dan siyasa mai karfi kamar Jibrin wanda yake dan asalin wannan jiha ta wadda APC ke da karfi a cikinta zai iya barin jam’iyyar a daidai wannan lokaci, lallai Tinubu na iya kasancewa a hanyar rasa farin jininsa a yawancin yankunan shiyar.
4. Tabbaci ne cewa babbar jam’iyyar adawa ta kasar za ta yi amfani da wannan rikicin gaba daya a kamfen dinta. Balle ma ace, idan Jibrin ya sauya sheka zuwa PDP, zai zama dabara kan dabara lokacin da gangamin kamfen din shugaban kasa zai fara sosai gabannin 2023.
5- Yemi Osinbajo na iya zama mafita na gaba. Duba ga yanayi da dama, Osinbajo ne babban dan takarar shugaban kasa na APC bayan Tinubu. Mataimakin shugaban kasar da kansa ya bayyana cewa Allah ya dora shi a kujerar mulki domin ya yi amfani da tarin gogewarsa idan ya zama shugaban kasa a 2023.
