Babu Gaskiya A Labarin Zan Tsaya Takara – Shugaban INEC

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar za?e mai zaman kanta ta ?asa, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya musanta rahoton dake yawo cewa da yuwuwar ya nemi takarar shugaban ?asa a 2023.

An ruwaito ?ungiyar marubutan kare ha??in ?an adam ta Najeriya, a ranar Lahadi, ta yi kira ga yan Najeriya ka da su ka?u idan suka ga shugaban INEC ya sayi Fom ?in APC miliyan N100m.

?ungiyar ta yi wannan tunani ne bayan ganin an saya wa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, Fom ?in nuna sha’awa da tsayawa takara a Jam’iyyar APC.

Amma da yake martani ta hannun Sakataren watsa labaransa, Rotimi Oyekanmi, ranar Lahadi, shugaban INEC ya bayyana cewa ba shi da sha’awar shiga takarar Kujerar Shugabancin kasa.

“Kiran da ake shugaban INEC ya shiga sahun takara a 2023,” Yakubu ya ce hakan ba zai ta?a yuwuwa ba. “An ja hankalin mu kan wasu karerayi da ake ya?awa a wani ?angaren Najeriya cewa ka da mutane su yi mamaki idan suka wayi gari shugaban INEC ya shiga sahun takarar shugaban ?asa ko rokon ya shiga.”

“Wannan ikirarin ya zarce hankali, ba zai ta?a faruwa ba. Shugaban hukumar za?e ya maida hankali wajen gudanar da sahihi kuma ingantaccen za?e ne kawai.”

Related posts

Leave a Comment