Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce za su “tabbatar ba a samu ?arancin ku?i ba” a gwamnatinsa wajen samar da tsaro a fa?in ?asar kuma “saura ?iris a samu nasara a ya?i da ‘yan ta’addan Boko Haram masu fakewa da Musulunci”.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake taya al’ummar Musulmi murnar bikin ?aramar Sallah a ranar Lahadi, yana mai cewa “muna da dalilin da ya sa za mu yi bikin (Sallah) cikin ?warin gwiwa”.
“Ya?in da ake yi da ‘yan ta’adda da suke fakewa da Musulunci ya kusa zuwa ?arshe,” in ji shi cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar.
“Ya?in ya ?auki lokaci kuma da wuya. Amma an kusa cimma nasara.”
