2023: Duk Ministan Da Zai Yi Takara Ya Ajiye Aiki – APC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jami’an gwamnatin na da zuwa ranar Asabar 30 ga watan Afrilu su ajiye mukaman nasu muddin suna da bu?atar tsayawa takara.

Matakin ya shafi wasu ministocin gwanatin Buhari kamar ministan sufuri Chibuike Rotimi Amaechi da kwadago Chris Nigige, suna ciki jami’an da suka bayana aniyarsu ta tsayawa takara.

Sashe na 3(i) na dokar jam’iyyar APC kan tsayar da ‘yan takara a zaben 2023 na cewa: “Ba a yarda wani jami’in da ke ri?e da mukami a kowane matakin gwamnati ya zama deleget ko a zabe shi domin fitar da ‘yan takara ba”

Related posts

Leave a Comment