Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya ce zai nemi takatar shugaban ?asa a za?en 2023 bayan shugaba Buhari ya amince masa ya yi hakan.
Rahotanni sun bayyana cewar Gwamnan ya gana da shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ranar Talata a Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.
Bayan ganawa da shugaban ?asan, Ayade ya ce Buhari ya bukace shi ya nemi shawarar mutane kan lamarin yayin da zai sa masa ido ya gani.
Game da ra?e-ra?in APC na shirin tsayar tsohon shugaban ?asa, Goodluck Jonathan, Ayade ya ce ya na matukar girmama shi, idan APC ta ?auki matakin ba shi takara zai goya masa baya.
“Ina da ya?inin shugabannin mu na jam’iyya zasu ?auki matakin da zai kai mu ga nasara, don haka idan kun fahimce ni, ni kawai ina ?aya daga cikin iyali ne, ina bayan Buhari, kuma ina neman takara.”
“A duk lokacin da jam’iyyar mu ta ga cewa Jonathan ne zai iya kaimu ga nasara, zan maida baki ?aya goyon bayana a kan sa na taimake shi.”
“Ba na siyasar ya?i, duk wanda ya san yadda na zama gwamna, na kai wannan matsayin ne saboda goyon bayan wanda gwamna ke so, sai a kai sa’a na zama nine ?an takara. Don haka zan koma bayan wanda shugaban ?asa ke so.”
