Rahotannin dake shigo mana daga Makurdi babban birnin Jihar Binuwai na bayyana cewar Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce shi kadai ne zai iya kwato wa jam’iyyar PDP mulki muddin aka ba shi takara a 2023.
Ya bayyana haka ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Jihar Binuwa, da ya gudana a ranar Lahadi.
Ya kuma shaida musu aniyarsa ta tsayawa takarar Shugabancin Kasa a hukumance, ya roki goyon bayan daliget din da su zabe shi.
“In dai ana son a kori PDP daga mulki, to ni ne zan iya nuna wa APC yatsa. Dole mu kwace mulkin nan, kuma a shirye nake.
“Ina bayyana aniyata ta tsayawa takara a karon farko a hukumance a nan jihar Binuwai. Zan tsaya takarar Shugaban Kasa”.
