Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewa ba zai janye wa Tinubu ba a yin takara, sai dai zai tausa jigon APC Bola Tinubu kuma ?an takaran shugaban kasa ya janye masa idan aka zo za?en fidda gwani na jam’iyyar APC.
Okorocha ya ce Tinubu babba ne, saboda haka zai tausa shi ya janye masa idan lokacin za?en fi dda gwani yayi
” Ni da Tinubu ne za mu kasance a kan gaba a za?en fidda gwani na shugaban kasa a APC. Amma kuma a lokacin zan tausa shi ya ci girma ya janye ya bar mini wurin ni in kwafsa da PDP.
” Ni mutum ne mai tausayin jama’a, bana yin ?abilanci. Musulmi ne kai, Kirista ne kai, Bahaushe, Inyamiri ko bayarabe, ni a wurina mutim kawai nake gani. Babu banbancin addini ko na kabila
Okorocha ya kara da cewa, shine ya ke tada kura a yankin kasar Igbo haka kuma shima Tinubu ne ke tada kura a yankin kasar Yarabawa. A dalilin haka kuwa su biyun ne za a fafata da su idan za?e ya zo.
A ?arshe ya roki ?a?an jam’iyyar su kakka?e katin zaben su kowa ya kwana ya kum tashi da shirin tunkarar babban za?e da ke zuwa.
” Kada ka saida ?ancinka, a tabbata ka yi zabe domin kanka da cigaban kasa Najeriya.
