Rahoton dake shigo mana daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa zai farfado da tattalin arzikin Najeriya tare da rage dogaro kan arzikin man fetur idan ya haye karagar mulki a 2023:
Dan takaran kujeran shugaban kasan ya ce ya yi niyyar gadar kujerar shugaba Muhammadu Buhari ne don amfanin yan Najeriya, amma ba domin biyan bu?atar kanshi ba.
Tinubu yace rashin wutar lantarki ne babban matsala ga cigaban tattalin arzikin Najeriya saboda rashin wuta ke kara farashin kaya, hana mutane aiki cikin nishadi, da kuma kawo tasku ga samar da ayyukan yi.
“Ingila, Amurka da China sun aiwatar da tsare-tsare don kare masana’antunsu, wajen samar da ayyukan yi, da fitar da kaya. Wadannan kasashe sun daura kansu kan turban nasara a yau da gobe.” “Wajibi ne mu yaki wadannan matsalolin dake hanamu samun ingantaccen wutan lantarki.
