Rahotannin daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Sarkin Kano na 14, kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya jinjina wa mabiya addinin da ba musulunci ba, saboda kar?ar da suka yi wa tsarin bankin Musulunci hannu bibbiyu.
Khalifan ya yi wannan jawabi a Legas ranar Lahadi, a lokacin da ya halarci taro matsayin sa na Babban ba?o na musamman a wurin taron ?asa na 5 don tattaunawa kan harkokin kasuwancin tsarin Musulunci, wanda masana da ?wararru musulmai suka shirya a Legas.
Taron mai taken: “Tsarin Banki da Kasuwancin Islama A Najeriya: Riba, ?alubale da Nasarori”, an gayyato masani kuma farfesan Shari’ar Muslunci a Jami’ar Ilorin, AbdulRazaq Alaro, a matsayin babban ba?o mai jawabi.
Sanusi wanda ya ha?aito tarihin kafa Bankin Musulunci a Najeriya, kuma ya bada labarin irin gwagwarmaya da sukar da tsarin ya sha daga bakin mutane daban-daban, har da shugabannin addinai, ya gode wa wasu da ba musulmai ba, saboda goyon bayan da suka bayar har CBN a lokacin mulkin sa ya fita daga tarkon duk wani ?alubalen da ya fuskanta.
