An Yabi Buhari Kan Dala Miliyan Guda Da Ya Ba Afghanistan

Babban sakataran kungiyar hadin kan musulunci (OIC), Hissein Brahim Taha, yayi jinjina bisa yadda Najeriya ta bai wa kungiyar kula da walwalar dan adam ta Afghanistan “Kyautar dala miliyan daya”.

A wata takarda da hedkwatar OIC ta fitar ta ce tallafin yazo daidai da lokacin kara wata sabuwar yarjejeniya ga kungiyar na kokarin ganin an kawo karshen halin da ‘yan adam suka fuskanta a Afghanistan, don taimaka wa wajen biyan bukatun miliyoyin mutanen kasar, wadanda suka hada da mata da yara.

OIC zata cigaba da mayar da hankali wajen nemo wa mutanen Afghanistan tallafi, sannan ba za tayi kasa a guiwa wajen kokari matuka don tabbatar da magance matsalar Afghanistan ba.

“OIC tana rokon duk kasashe, masu mukamai da masu ruwa da tsaki da su zo su bada gudunmawar su ga kungiyar kula da walwalar bil adama ga Afghanistan ta asusun bankin daga cikin bankunan musuluncin da aka tanadar domin hakan (IsDB),”

Related posts

Leave a Comment