Rashin Tsaro Na Iya Haifar Da Kalubale A Zaben 2023 – Kungiyar CAN

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?ungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bayyana cewa zaben 2023 da ake ta shirye-shirye da zumu?in zuwansa ka iya zama mara inganci.

Kungiyar ta ce matsalar tsaro da yan ta’adda, yan bindiga da masu garkuwa suka jefa Najeriya shi ne, “babban barazana” ga zaben 2023 dake tafe.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Laraba, 2 ga watan Maris, 2022, ta nuna cewa shugaban CAN, Dakta Samson Ayokunle, ya yi wannan furucin ne yayin gana wa da wakilan kungiyar tarayyar turai (EU) a Abuja.

Ayokunle, wanda yana ?aya daga cikin shugabannin majalisar ha?in kan addinai, ya ce yanayin tsaro ka iya shafar sahihanci da ingancin zaben dake tafe lamarin da zai iya dagula komai.

Haka nan ya yi bayanin cewa matsalar da ?asa ke ciki game da tsaro ba zata bar mutane su fita runfunan za?e ba, saboda tsoron garkuwa, cutarwa ko kisa. A cewar shugaban CAN, “Alamu sun nuna gwamnati na fa?i tashin da?ile yanayin mara kyau, kokarin da suke a yanzu bai kai ya kawo ba.”

Bisa haka, Ayokunle ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su tashi tsaye su kawo ?arshen ya?uwar matsalar tsaro a Najeriya. A kalamansa ya ce: “Idan haka ta cigaba da faruwa, masu ka?a kuri’u da yawa ba zasu fito ba, saboda haka sakamakon za?en ba zai zama gamsasshe ba.”

Rabaran Ayokunle ya yi kira ga hukumar za?e INEC kada ta tsoma kanta cikin harkokin siyasa yayin gudanar da aikin dake kanta. Ya kuma bukaci mambobin hukumar INEC da suke yan amshin shatan jam’iyya mai mulki su gaggauta yin murabus ko a fatattake su domin gudun yin magudi.

Related posts

Leave a Comment