Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 11 Da Kona Gidaje 30

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar a?alla mutum 11 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ?aramar Hukumar Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna.

Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta Jihar Kaduna ce ta tabbatar da hakan inda ta ce an kai harin ne a Kurmin Masara da ke Zangon Kataf ?in da safiyar Lahadi.

Bayan mutanen da aka kashe, akwai wa?anda aka tabbatar da cewa sun samu raunuka haka kuma an ?ona sama da gidaje 30.

Gwamnatin Kadunan ta ce sojojin sama da suka yi ?o?arin kai ?auki an yi musu kwanton ?auna a hanyarsu ta zuwa wurin da lamarin ya faru.

Sai dai sojojin sun samu galaba kan wa?anda suka yi musu kwanton ?auna tare da dakarun Operation Safe Haven domin isa Kurmin Masara.

Related posts

Leave a Comment