Nasarar Mulkin Buhari Ya Zarce Shekaru 16 Na PDP – Minista

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya yi i?irarin cewa ayyukan da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi na raya ?asa, sun zarce ayyukan da gwamnatin PDP ta yi yawa a cikin shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulki.

Ya yi wa mulkin PDP ku?in-goro, inda ya ce gaba ?aya mulkin shugabannin PDP ?in uku da aka yi ya ke nufin cewa ayyukan su a jimlace ba su kai ayyukan Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Fashola ya yi wannan i?irarin ne a yayin da ya ke jawabi wurin wani taron tattauna batun dangantakar gwamnati da al’umma a aikace.

Wasu gidajen radiyo a Kano dai sun ri?a watsa shirin kai-tsaye, inda wasu jama’a su ka samu damar ganawa da ministan a kan batun mulkin da su ke kai.

A wurin taron dai Fashola ya ri?a nuna wasu hotunan ayyukan da Gwamnatin Buhari ta yi, kuma ya na nuna irin yadda jama’a ke yabawa da ayyukan. Duk ya yi haka ne domin ya nuna irin gagarimin aikin inganta rayuwar al’umma da wannan gwamnatin ta aiwatar a cikin shekaru shida ka?ai, duk kuwa da cewa ku?a?en da Gwamnatin APC ta samu ko ka?an ba su kamo ?afar ku?a?en da Gwamnatin PDP ta samu a cikin shekaru 16 ?in mulkin ta ba.

“Yi wa al’umma ayyukan raya ?asa ita ce halastacciyar hanyar da za a raba ku?i a cikin tattalin arziki daga hannun gwamnati can daga sama zuwa ?asa.”

Minista Fashola dai shi ne Ministan Ayyuka tun daga hawan APC mulki cikin 2015 har zuwa yau.

“Tsawon shekaru shida kenan da suka gabata tuni wannan gwamnatin ta na yin abin da gwamnatin Amurka ke ?o?arin ta ga ta yi. Wato batun amincewa da kudirin dokar gina ayyukan raya ?asa. Kuma har yanzu ana sa-toka-sa-katsi kan wannan kudirin a Majalisar Amurka.”

Fashola ya kuma ?i yarda da masu cewa wai da APC da PDP duk ?aya ne a yanzu. Ya ce ba ?aya ba ne, duk da dai wasu ‘yan PDP ?in sun fice sun koma cikin su Fashola a APC.

“Damar da PDP ta samu har ta tsawon shekaru 16 domin ta yi wa ‘yan Najeriya aiki, amma ba ta yi ba. Sai ga shi mu APC mun yi ayyukan da PDP ta kasa yi cikin damar da muka samu ta shekaru shida ka?ai.

“To ko ta fannin inganta rayuwar al’umma ?in nan da muke yi a fa?in ?asar nan, ai mun bambanta da PDP. Ballantana ma ba bambanta ka?ai muka yi ba, mun zarce su fintinkau.” Inji Fashola.

Yayin da ya ri?a lissafa ayyukan titina da gadoji a fa?in ?asar nan, Fashola ya ?ara da cewa “yanzu haka ana ci gaba da gina gidaje a jihohi 34 da Abuja. Sannan kuma ana gina Sakateriyar Gwamnatin Tarayya a jihohin Anambra, Nasarawa, Bayelsa, Zamfara, Osun da Ekiti.”

Related posts

Leave a Comment