Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Matar Wanda Ake Zargi Da Kisan Hanifa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Kotu ta umarci ‘yan sanda su ci gaba da tsare Jamila Muhammad, matar mutumin da ake zargi da kisan Hanifa Abubakar mai shekara 5 a Jihar .

Ana zargin Jamila mai shekara 30 da ha?a baki wajen ?oye yarinyar da mijinta Abdulmalik Tanko ya sato, da ?ulla makirci, da sace mutum, da kuma kisan kai.

Da yake karanto tuhumar da ake yi mata, lauya mai shigar da ?ara ya ce ana zargin ta da ?oye wadda aka yi garkuwa da ita tsawon kwana biyar.

Jamila ta ?aryata rahoton farko da aka bayar wanda ya zarge ta da ?oye Hanifa a gidanta.

Idan ba a manta ba, Abdulmalik ya fa?a wa ‘yan sanda cewa bayan ya sace Hanifa ya kai ta wajen matarsa ne, inda ta zauna a gidan kafin daga baya ya kashe kuma ya binne ta a farfajiyar makarantarsa da ke Kwanar Dakata ta ?aramar Hukumar Nasarawa a birnin Kano.

Kotun Majistaren da ke Gidan Murtala ta ?age zaman zuwa 2 ga watan Fabarairu tare da uamrtar ‘yan sanda su ci gaba da tsare Jamila.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ce a shirye yake ya sanya hannu kan zartar da hukunci idan kotu ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa.

Related posts

Leave a Comment