Na Yi Nasarar Magance Matsalar Tsaro A Najeriya – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya jajirce cewa gwamnatin sa ta da?ile gagarimar matsalar tsaro a ?asar nan.

Haka dai shugaban ya nanata a hirar da aka yi da shi a ranar Laraba, a gidan talabijin na Channels. Premium Times ta saurari tattaunawar a tsanake.

Wannan i?irarin na Buhari ya zo ne a daidai lokacin da ake ta bindige ‘yan Najeriya a ko’ina cikin sassan ?asar nan.

Banda yawaitar kashe-kashe da ake yi, a kullum ana yin garkuwa da ?imbin matafiya ko a yi tattaki har gida a kama mutum a yi awon-gaba da shi.

?aruruwan jama’a sun ri?a gaganiyar tara ku?a?en kar?ar fansar wa?anda aka yi garkuwa da su.

“Idan za ku iya tunawa, lokacin da na ke ya?in neman za?e cikin 2015, abubuwa uku ne na ri?a ?aukar al?awarin magancewa. Wato rashin tsaro, tattalin arziki da kuma ya?i da cin rashawa. To kuma idan ‘yan Najeriya za su yi adalci, sai su yi waiwaye su tuna halin da ?asar nan ke ciki a 2015 da kuma yadda ta ke a yanzu.

“Duk wanda ke Barno da Yobe da Adamawa, zai tabbatar maka cewa an samu ci gaban tsaro sosai a yankin Arewa ta Gabas da Arewa ta Tsakiya.” Inji Buhari

Mulkin Najeriya: Na Yi Bakin ?o?ari Na -Buhari:

Duk da halin dagulewar matsalar tsaron da ake fama da ita a fa?in ?asar nan, sai kuma halin ?uncin rayuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi dai batun mulkin Najeriya ya yi bakin ?o?arin sa.

Buhari ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na NTA, wanda aka nuna a ranar Alhamis da dare.

An nuna wannan hira ce kwana ?aya bayan nuna tattaunawar da Channels ta nuna, wadda gidan talbijin ?in mai zaman kan sa ya yi da Buhari ?in a ranar Laraba.

Shugaba Buhari ya ce shi dai ya san ya yi bakin ?o?arin sa. Saboda haka ya na fata da ro?on ‘yan Najeriya su ri?a tuna shi bayan ya sauka a matsayin wanda ya yi wa ?ara aiki tu?uru bakin ?o?arin sa.

Buhari ya ce idan ya sauka zuwa zai yi ya huta kawai, bayan watanni 17 ?in da suka rage masa.

“Abin da na ke jira na ji ‘yan Najeriya su na fa?i bayan na sauka, shi ne su ri?a cewa ‘ai mutumin nan ya yi bakin ?o?arin sa.

A tattauanawa da Channels ne Buhari ya ce matasa su daina tunanin yin ilmi don samun aikin gwamnati.

Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci matasan Najeriya cewa su yi watsi da tsohuwar al’adar yin ilmi don a samu aikin gwamnati.

Da ake tattaunawa da shi a Gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba da dare, Buhari ya ce yin ilmi ba wata hanya ba ce garanti da matashi zai ce sai ya samu aikin gwamnati.

“Ina fatan idan matasa je makarantu, idan sun yi ?o?ari sun samu ilmi har sun samu digiri, to su daina tunanin sai sun yi aikin gwamnati.

“Ka daina dogaro da gwamnati ta ba ka aiki idan ka yi ilmi. Shi ilmi ana yin sa ne don mutum ya fayyace hanyoyin da zai warware wa kan ka matsalolin rayuwa. To ta nan ne za ka fi marar ilmi tunani.” Inji Buhari.

“Tsohuwar ?abi’a ce tun ta zamanin mulkin Turawa, lokacin ne ake tunanin a yi ilmi don a samu aikin gwamnati, a mallaki mota.”

Najeriya na fama da matsalar yawan marasa aiki, kamar yadda ?ididdigar Hukumar ?ididdigar Al?aluman Bayanai (NBS) ta sha bayyanawa.

A ?arshen shekarar 2020, NBS ta ce kashi 33.3 na ‘yan Najeriya masu ?arfin iya yin aiki, ba su da aikin yi. Wato kusan matashi miliyan 23.3 kenan, ko kuma kashi 1 bisa 3 na su.

Cikin watan Yuni 2021, ne kuma Ministan Wasanni Sunday Dare ya ce za a bu?e rajistar neman aiki ga matasan Najeriya.

A wancan lokacin dai Ministan Harkokin Matasa da Wasanni, Sunday Dare, ya bayyana cewa zai shige a gaba domin tabbatar da cewa an bude rajistar matasa marasa aikin yi a kasar nan.

Wannan rajista da za a bude, Dare ya ce za ta saukake wa matasan kasar nan hanyoyin nema da samun aiki.

Ya ce tunanin bude rajistar ya biyo bayan kisan da aka yi wa wata matashiya a yayin da ta fita neman aiki a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a makon da ya gabata.

Yayin da ya ke mika ta’aziyya da jimamin rashin matashiyar mai suna Iniobang Umoren ga iyayen ta, Dare ya ce babban abin bakin ciki ne da tsananin tausayi kisan yarinyar, wadda wani mai suna Akpan ya yi.

Sannan kuma ya gode wa kawayen yarinyar da sauran jama’ar da su ka yi matukar kokarin fallasa wanda ya kashe ta.

Ministan Matasa Wasannni ya ce, “zan jagoranci hakilon ganin an bude Rajistar Tattara Sunayen Matasa Marasa Aiki, wadda za ta kasance a karkashin Rajistar Kididdiga ta Kasa.

A Najeriya dai ana fama da rashin aiki, inda cikin 2030 Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa, NBS ta ce rashin aikin yi ya kai kashi 33.3.

Lamarin ya kara tsanani ne saboda shi ma malejin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci sun kara cillawa sama.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da su ka fi fama da marasa aiki da zauna-gari-banza a duniya.

Related posts

Leave a Comment