Babu Maganar Sulhu Tsakanina Da Ganduje – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta wasu ra?e-ra?i da ke yawo da ke bayyana cewa yana tattaunawa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje don yin sulhu.

Yayin wata hira da Channels TV da yammacin ranar Lahadi. Kwankwaso ya ce ya ji da?in ziyarar ta’aziyyar da Ganduje ya kai masa kwanakin baya, amma bayan wannan ziyara ta gaisuwa babu wata magana da ake yi a bayan fage dangane da yin sasantawa.

Ya hakaito yadda ala?arsa ta kasance da Gandujen a baya tun lokacin da ya yi mata mataimakin gwamnan Kano a za?en 1999, da kuma yadda suka ci gaba da aiki tare har zuwa 2015 lokacin da suka raba garin bayan ya zama gwamna.

An tambaye shi cewa to shin yanzu idan ka samu wata dama za ka sake bayar da sunan Ganduje kamar yadda ka yi a baya ?.

Sai ya kada baki ya ce ”A yanzu dai ka san ba a jam’iyya ?aya muke ba, don haka ina ga babu ma bu?atar yin wannan tambaya, don haka ko da dama ta samu akwai mutanen da suka cancanta cikin wa?anda nake tare da su”.

Related posts

Leave a Comment