Allah ya yi wa kwararren dan Jaridar nan, Alhaji Wada Maida rasuwa a daren jiya Litinin, bayan yar gajeruwar rashin lafiya. Wanda kafin rasuwar sa shi ne Mawallafin Jaridar nan ta Turanci da ake bugawa A Abuja (People’s Daily) Kuma shi ne Shugaban Kwamiti Kula Da Kamfanin Dillancin Labarai Nijeriya wato (NAN) har ila yau, yana cikin masu hannun jari a Jaridar (Daily Trust)
Zaa yi sallah zanaidarsa a yau Talata da misalin karfe daya na rana,a masallacin Area 1, za’a rufe shi a makabartar Gudu da ke Abuja.
Alhaji Wada Maida, dan asalin Jihar Katsina, yana da Shekaru sabain da haihuwa. Ya bar Mata da ‘yaya da jikoki.
Allah Ya Jikansa da Rahama
