Da Dumi-Dumi: An Damke Bakin Haure Cikin ‘Yan Bindiga

Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta ce Sojojin Operation Whirl Stroke a Jihohin Benuwai, Nasarawa da Taraba sun kama ba?in-haure 16 da su ka tsallako daga Jamhuriyar Nijar su na kai hare-hare.

Sanarwar ta ce an kama su a wurare daban-daban cikin jihohin tsakiyar Najeriya.

Daraktan Ya?a Labarai na Hukumar Tsaron Najeriya Burgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya yi wannan ?arin haske a ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya ke ?arin haske dangane da nasarorin da dakarun Najeriya ke ci gaba da samu a yankunan ?asar nan daban-daban.

Related posts

Leave a Comment