Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya na bu?atar a zuba mata Naira tiriliyan 348.1 domin ta cimma nasarar Shirin Bun?asa ?asa na 2021-2025.
Buhari ya yi wanann bayanin a ranar Laraba, lokacin da ya ke ?addamar da shirin na National Development Plan na Shekaru Biyar.
Shirin dai ya zama ?orawa ce zuwa mataki na gaba, daga Shirin Farfa?o Da Tattalin Arzikin ?asa na 2017-2020, wanda wa’adin sa ya ?are cikin Disamba, 2020.
Buhari ya ce ana bu?atar zuba wannan jari na Naira tiriliyan 348.1 a cikin tattalin arzikin Najeriya, domin a samu ya bun?asa da kashi 5 bisa 100 a tsawon shekaru biyar ?in 2021-2022.
