Tabarbarewar Tsaro: Masana Sun Gano Bakin Zaren

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tawagar masana da ta jagoranci taron neman mafita ga matsalar tsaro ta fitar da shawarwarin da take ganin ya kamata gwamnatin Buhari ta yi aiki da su domin samun mafita.

Tawagar wadda tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya jagoranta tare da hadin kan tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar da Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III da kuma Dr Gumi da Bishop John Onaiyekan ta gudanar, na kwana uku domin lalubo bakin zaren kan matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

?aya daga cikin mahalarta taron Dr Hakeem Baba Ahmed ya bayyana matsayar da aka cimma bayan zaman.

“Taron ya ba Buhari shawarar ya ?ara tausayi da bu?e ?ofarsa don sauraren shawarwari da damuwar ?an Najeriya.

“Mun kuma ba da shawarar a bi duk hanyoyin da suka kamata a kawo ?arshen kashe-kashe a Najeriya, wanda ya ha?a da sauraren masu aikata laifin da ke cewa akwai dalilin da ya sa suke ta’addanci.

Related posts

Leave a Comment